
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da babban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kai ɗaukin gaggawa, Mohammed Hamdan Dagalo yayin da ake ci gaba da kafsa faɗa tsakanin dakarun shugabannin biyu na Sudan.
Kimanin 185 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar faɗan ranar Asabar.
Anthony Blinken ya wallafa wani saƙon Tuwita da ke cewa yana jaddada buƙatar gaggawa ga dakarun shugabannin biyu su tsagaita.
Ya nanata cewa muhimmancin haka shi ne a tabbatar da tsare lafiyar jami’an diflomasiyya da kuma ma’aikatan ba da agaji.
Rundunar jami’ai masu kayan sarki ta RSF ta amsa cewa an yi wannan tattaunawa ta wayar tarho da Mista Blinken a shafinta na sada zumunta sai dai ba ta bayar da wani tabbaci na kawo ƙarshen zaman gabar ba.
Ba a iya mutunta wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa’a uku da aka sa ba daren Litinin, inda kowanne ɓangare yake zargin ɗan’uwansa da alhakin keta yarjejeniyar.
An ci zarafin wani jami’in diflomasiyyar Tarayyar Turai a gidansa na aiki, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an yi harbi kan gine-ginen hukumominta da gidajen ajiyar kaya da masaukan baƙinta kuma wawashe su.
An fasa gidajen wasu fararen hula kuma an far wa magidanta, sai dai rundunar RSF ta musanta hannun dakarunta.
Shugabannin sojin biyu sun kasa amincewa kan makomar Sudan, ciki har da batun shigar da dakarun RSF cikin rundunar sojin ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Ana ci gaba da faɗa tsakanin dakarun rundunar RSF da kuma sojojin Sudan