Amurka ta Gargadi Shugaba Buhari Game Da ‘Operation Crocodile Smile’ a Niger Delta


 

Kasar Amurka ta gargadi shugaba Muhammadu Buhari game da salonsa na kawar da rikici a Nijeriya musamman ma a yankin Niger Delta inda sojin kasar suka kaddamar ta sabon ofireshon mai suna Crocodile Smile (Murmushin kada).

Wannan ya zo ne a sakamakon ci gaba da ake samu na kiraye kiraye daga kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya da ke cewa shugaba Buharin har yanzu bai fahimci mecece demokradiyya ba.

Amurka ta sanar da shugaban matsayarta ta ne ta bakin jakadanta a Nijeriya, ambasada David Young, wanda ya yi kira ga Buhari da ya yi amfani da hanyoyin sulhu ko tattaunawa wajen kashe rikicin.

Ya kara da cewa gwamnati ta fito da hanyoyin bunkasa rayukan mutanen yankin Niger Delta ta yadda za’a kauda laifuka da ta’addanci.

You may also like