Amurka ta haramta amfani da wayar Samsung.  


Hukumomin Amurka sun gargadi masu amfani da sabuwar samfurin wayar salula ta Samsung su daina amfani da ita, kuma su kashe saboda wasu da dama batir din su ya kama da wuta.
Hukumar kare haƙƙin masu ma’amala da kayan da kamfanoni suka ƙera ta ce, ta soma tattauna da Samsung domin a soma janya wayar Galaxy Note 7 ba tare da ɓata lokaci ba.

Yanzu haka dai kamfanin na Samsung yana janye wayar miliyan biyu da rabi daga duk fadin duniya.

India ta shiga sahun kasashen da aka haramta amfani da wayar Galaxy Note 7.

Ranar Alhamis ne dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Amurka ta haramtawa fasinja amfani da wannan samfurin wayar acikin jirgin sama.

You may also like