Amurka Ta kaKaba Wa Iran Sabon TakunkumiSabon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya kakaba wa kasar Iran sabon takunkumi bayan wani gwajin makami mai linzami da Iran a kwanan nan.
Wannan takunkumin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama ta yi nisa wajen dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Da yake jaddada matsayinsa kan takunkumin, Donald Trump ya nuna cewa gwamnatin Iran ba ta fahinci yadda Obama ya saukaka mata ba ne inda ya nuna cewa ba zai lamunci duk wata barazana daga Iran ba.

You may also like