AMURKA TA KOKA KAN YADDA DUNIYA TA JUYA MATA BAYA KAN BIRNIN KUDUSGwamnatin Amurka ta koka kan yadda kasashen duniya suka juya mata baya kan matsayin da ta dauka na amincewa da birnin Jerusalem a matsayin Babban birnin kasar Isra’ila.

A jiya Alhamis ne, zauren Majalisar Dinkin duniya, kasashen duniya suka kada kuri’a kan matsayin birnin Jerusalem inda kasashe 128 suka goyi bayan a raba birnin gida biyu a tsakanin Falasdinawa da Isra’ila yayin da kasashe 9 suka goyi bayan Amurka wadda ta mika birnin ga Isra’ila.

Jakadan Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta ce Amurka ba za ta taba mantawa da wannan rana ba wanda kasashen duniya suka caccake ta don kawai ta bayyana matsayinta kan wani al’amari a matsayinta na ‘yantacciyar kasa.

You may also like