Amurka ta mayar wa Masar wani akwatin gawa na zamanin Fir’auna



Akwatin mai tsawon mita 2.9 (ko kuma kafa 9.5)  mallakin wani malamin coci ce da ake kira Ankhenmaat

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Akwatin mai tsawon mita 2.9 (ko kuma kafa 9.5) mallakin wani malamin coci ce da ake kira Ankhenmaat

Amurka ta mayar wa dasar wani akwatin gawa da aka sassaka da dutse, wanda Amurkar ta ajiye a gidan kayan tarihinta.

Akwatin mai tsawon mita 2.9 (ko kuma kafa 9.5) tun na zamanin mutanen baya, da masarautar Fir’auna, wanda wani malamin coci da ake kira Ankhenmaat ya mallaka shekara 664 zuwa 332 kafin haihuwar annabi Isa.

An sace akwatin daga makabartar Abu Sir da ke arewacin Masar a 2008, wanda wani kamfanin bibiyar kayayyakin tarihi ya ɗauke kuma ya bi da shi ta cikin Jamus zuwa Amurka.

Wanda aka bai wa akwatin ya karɓe shi ne a matsayin aro kuma ya ajiye shi a gidan tarihi na (Houston Museum of Natural Science ) a 2013.



Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like