
Asalin hoton, National Archive
A karon farko, an fitar da mafi yawa cikin takardun hukuma sama da 16,000 na bayanai game da kashe Shugaban Amurka John F Kennedy a 1963.
Shugaba Biden ne ya ba da umarni ga Hukumar Adana Bayanai ta Amurka ta fitar da cikakkun takardu kashi 70% a cikin takardu dubu goma sha shida, kan batun kashe John F Kennedy
Fadar White House ta ce fitar da kashi 70 na takardun ba tare da rufe komai ba, za ta bai wa jama’a gagarumin haske da fahimta kan binciken gwamnati cikin wannan mummunan al’amari a tarihin Amurka.
Shekara 59 ke nan tun bayan harbe Kennedy a Texas, kuma har yanzu akwai ragowar kashi 30 na bayanai da gwamnatin Amurka ba ta fitar ba.
Wata dokar fayyace gaskiya ta 1992 ce ya kamata ta tilasta sakin takardun a shekarun da suka wuce amma Hukumomin CIA da FBI da sauransu suka yi ta fafutukar ci gaba da sirrata bayanan.
Sama da rabin ƙarni bayan harbe Shugaba Kennedy a kwambar motocinsa – ƙuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa mafi yawan Amurkawa sun yi imani gwamnati na rufa-rufa game da mutuwarsa.
Jinkiri ba ƙaƙƙautawa wajen fitar da bayanan ya rura gagarumar da’awar ƙullin maƙarƙashiya tsawon shekaru gommai.
Ko da yake, sannu a hankali an fitar da takardu da dama game da kisan gillar tun bayan 1963, amma ba dukkansu ne ba.
Shugaba Biden a yanzu ya ba da umarni sakin cikakkun takardu kashi 70 a cikin dubu goma sha shida, waɗanda a baya an fitar da su ga jama’a, ko da yake an rufe wasu sassa.
Ya riƙe ragowar ne saboda dalilan tsaro, inda ya ce har yanzu ana nazarin su.
Masana tarihi za su yi fushi da hakan – ko da yake suna fata waɗanda aka saki za su ƙunshi ƙarin bayanai game da mutumin da ya aikata kisan Lee Harvey Oswald.
Mutane da yawa sun yi imani CIA ta san abubuwa masu yawa fiye da yadda hukumar ta ce ta sani a hukumance game da Lee Oswald- wanda ya yi ƙoƙarin sauya sheƙa zuwa Tarayyar Sobiyet kafin mutuwar Kennedy.
Zuwa yanzu dai babu wata bankaɗar ban mamaki…kamar a ce ba Oswald ne mutumin da ya yi kisan ba.