Amurka Ta Sanya Dan Ben Laden, Cikin Jerin Mayan ‘Yan Ta’adda


4bk720d571560fa1dv_800c450

Amurka ta sanya sunan Hamza Ben Laden daya daga cikin ‘ya yan Ben Laden a cikin jerin sunayen mayan ‘yan ta’adda na duniya.

Shi dai Hamza Ben Laden ya jima yana yi wa Amurka da mutanen ta barazana, inda ko a watan Yuli daya gabata ya fitar da wani sakon sauti dake dauke irin wannan barazana.

A bayanin hukumar leken asirin Amurka ta fitar ta ce Hamza Ben laden na matukar sha’awar zama dan jihadi.

Kuma hakan a cewar bayanan hukumar ta CIA ta dau wannan matakin ne bayan da kungiyar Al-Qaida ta sanar a watan Agusta shekara 2015 cewa daga yanzu matashin Hamza yana daga cikin gungun ‘yan Jihadi.

Matakin dai ya tanadi toshe duk wasu kaddarori da duniya na Hamza Ben laden a Amurka, haka kuma an harmatawa duk wani ba’amurke yin mu’amular kasuwanci da saurayin dan shekaru kimanin 20.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like