Amurka ta yabawa Najeriya bisa yaki da Ta’addanci. 


Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da ke ziyara a Najeriya, ya ce abin farinciki ne yadda kasar ta samu kwato da yankuna da dama da suka fada hannun Boko Haram.
Mista Kerry ya taya Najeriya murna kan nasarar da take samu a yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram,sai dai ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mahukuntan da su yi taka tsatsan kada a wuce makadi da rawa da sunan yaki da ta’addaci.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriya Kerry, ya ce abin farinciki ne yadda Najeriya ta samu dama ta maido da yankuna masu yawa da suka fada hannun Boko Haram, sannan an samu dama ta kubutar da dubban mutane da ‘yan ta’addar suka yi garkuwa da su.

Ya ce Najeriyar da makobtanta sun taka muhimmiyar rawa wajen kashe kaifin ayyukan ta’addancin na Boko Haram, sai dai ya ce a yi taka tsantsan da dokoki na kare hakkin bil Adama idan hannun mahukunta ya kai ga ‘yan ta’addar da ma masu ikirarin neman ‘yancin yankin Biafra.

You may also like