Kasar Amurka ta bayyana cewa, matukar Rasha ba ta daina kaddamar da hare-hare a birnin Aleppo ba, to lallai za ta katse tattaunawar zaman lafiyar Syria.
A wata hira da ya yi ta wyar tarho da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, sakaten harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce, Amurka ta dora wa Rasha laifin amfani da munanan bama-bamai wajen kai hare-haren a birnin Aleppo.
Tuni dai Amurka ta fara shirye-shiyen katse tattaunawar zaman lafiyar Syria kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a yau.
Tun lokacin da karshen wa’adin yarjejeniyar tsagaita musayar wutar Syria a cikin makon jiya, birnin Aleppo ya gamu da hare-haren sama, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka tare da raunata jama’a.