Amurka Zata Girke Sojojinta 500 A Jihar Borno


A wata ziyara da mataimaki na musamman a majalisar dokokin Amurka Mr Mark Joy ya kai Jihar Borno ya tabbatar da cewa shugaban kasar Amurka Donald Trumpya amince sojojin kasarsa kimanin 500 su kai gudunmawa Jihar Borno cikin wannan wata mai karewa.

Mr Mark Joy ya tabbatar da hakan ne a yayin da ya ke jawabi wajen taron kaddamar da wata Kungiya mai suna AMR ORGANAZITION a jihar Borno.

Mr Mark ya kara da cewa gwamnatin kasarsa za ta sanya hannu wajen fatattakar ‘yan ta’adda daga Arewacin Nijeriya ta hanyar aiko da jirage marasa matuka guda takwas da motoci guda goma.

Mr Mark ya ce, ba mamaki rundunar da kasar Amurka za ta aika ya fi 500 din da ake fada.

Mr Mark Joy ya ce rundunar sojojin na Amurka za ta zo da wasu kayan aiki na leken asiri tare da kuma nunawa rundunar sojojin Nijeriya wasu dabarun sirri da za su kai ga cim ma nasarar samar da tsaro.

You may also like