Amurkawa Sunyi Zaben Tumun Dare – Abubakar Shekau


Shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar Boko Haram biyu da ake da su a Najeriya ya ce ko da Hillary Clinton Amurkawa suka zaba a zaben shugaban kasa na makon jiya sun yi hasara.
A cikin wani sakon murya da wani makusancinsa ya aiko wa sashen Hausa na BBC, Abubakar Shekau ya ce a shirye suke su kalubalanci manufofin zababben shugaban na Amurka.
Ya kuma yi Allah-wadai da matakin da ya ce sarkin kasar Saudiyya mai bin tsarin shari’ar musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr. Trump.
Ya yi amfani da wannan damar wajen daukar alhakin kai munanan hare-hare kan dakarun Najeriya a wasu sassan jihar ta Borno a kwanannan wanda ya hallaka da dama daga cikinsu.

You may also like