
Asalin hoton, Getty Images
Wata mace ‘yar ƙasar Sudan da aka tuhuma da yin zina ta tsallake rijiya da baya daga hukuncin kisa, amma duk da haka za ta yi zaman gidan yari na wata shida bayan ta amsa cewa ta sumbaci wani.
Da farko an yanke wa matashiyar ‘yar shekara 20 hukuncin kisa ta hanyar jefewa, lamarin da ya janyo terere daga ƙasashen duniya.
‘Yan sanda ne suka kama ta bayan kawunta ya kashe saurayinta.
Cibiyar Nazarin Harkokin Shari’ah da Zama Lafiya ta Afirka (ACJPS) ta bayyana hukuncin farko a matsayin wani “gagarumin karan tsaye ga dokar ƙasashen duniya”.
Wata kotu a birnin Kosti cikin jihar White Nile ce ta yanke wa bazawarar hukuncin kisa bayan samun ta da laifin yin zina.
Sai dai bayan taƙaddamar da aka yi ta yi a ƙasashen duniya, kotu ta sake sauraron shari’ar. Inda daga bisani, alƙalin kotun ya canza tuhumar da aka yi wa matar daga “zina” zuwa wata “baɗala” abin da ke nufin matar za ta yi zaman gidan yari saboda laifin da ta aikata.
Ta dai amsa a kotu cewa ta keɓe da wani mutum kuma ta ce sun sumbaci juna.
Lauyarta Intisar Abdullah ta ce alƙalin “ba shi da zaɓin da ya wuce ya ɗaure ta”.
“Matsalar ita ce ta amsa da bakinta a kotu cewa ta keɓe da namiji, tana cike da ƙuruciya, ba ta san sarƙaƙiyar shari’a irin wannan ba,” lauyar ta faɗa wa BBC.
Da farko an ba da belin matashiyar amma yanzu ta tafi gidan yari inda za ta fara zaman hukuncin da aka yi mata.
Cibiyar ACJPS ta ce ba a bai wa bazawarar lauya a shari’ar farko ba kuma an samu kura-kurai kan ƙa’idojin shari’ah da aka gindaya, lamarin da ya sa aka rushe hukuncin da aka fara yanke mata na jefewa.
Har yanzu Sudan tana amfani da hukuncin kisa kan wasu laifukan keta iyakokin Allah – laifukan da Allah a cikin Qurani mai Tsarki ya ambace su, ciki har da sata da kwartanci.
A tsarin dokokin Sudan, ana zartar da hukunce-hukunce kamar na bulala da yanke hannuwa da ƙafafuwa da rataye mai laifi ko jefe shi.
Mafi yawan hukunce-hukuncen jefewa a Sudan – sun fi faɗa wa kan mata ne – waɗanda kuma Babbar Kotu takan rushe su idan an ɗaukaka ƙara.
Sudan na ƙarƙashin mulkin sojoji tun bayan wani juyin mulki a shekarar 2021.