Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniya da kamfanin jiragen sama na Med-View kan kwaso ‘yan Nijeriya har su 5,037 da suka makale a kasar Libya.
Gwamnati dai ta yanke shawarar kwashe ‘yan Nijeriya daga Linya ne sakamakon rahotannin cin zarafin da ake yi masu kasar ta hanyar sayar da su don aikin bauta.