Rahotanni daga jihar Taraba sun tabbatar da cewa kimanin Shanu 300 ne aka arce da su a sabon rikicin da ya barke a karamar hukumar Sardauna da ke jihar Taraba.
Wasu daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su sun nuna cewa kimanin mutane 20 suka rasa rayukansu bayan hare haren da ‘yan dabar yankin suka kai kan makiyayan Leme.