An Bankawa Gidan shugaban ‘Yan Shi’a Wuta


 

Matasa Sun Kona Gidan Shugaban ‘Yan Shia Dake Zango Road, Tudun Wada, A Jihar Kaduna
….yayin da jami’an tsaro suka kashe mabiya Shi’a sama da goma a jihar Katsina
Wadansu Matasa da ba’a san ko su wanene ba sun kona gidan Mukhtar Sahabi, wanda shine shugaban ‘yan Shi’a a jihar Kaduna.
Kawo yanzu dai komai ya lafa a unguwan inda jami’an tsaro suka zagaye unguwan.

Tun jiya ne dai ake zaman dar dar a unguwan Zango da ke Tudun Wada, Kaduna.
A garin Funutua kuma dake jihar Katsina bayan masu zahara sun fito a safiyar yau, a yunkurin hana su da jami’an tsaro suka yi, kimanin mutane goma sun rasa ransu daga cikin mabiya Shi’an wadanda suka hada maza da mata.

You may also like