An Barke Da Dambarwar Wanda A Ke Hasashen Ya Lashe Zabe A Zamfara
Lawal ya yi zargin APC na neman tursasa jami’an zabe don sauya alkaluma a sauran kananan hukumomin da ba a gama baiyana sakamakon su ba.

Zargin na zuwa daidai lokacin da kwamishinan labaru na hukumar zabe Festus Okoye, ke cewa an samu wasu ‘yan siyasa a wasu jihohi da ke amfani da ‘yan banga don hargistsa zabe, kuma hakan ne ma ya sa soke zabe a wasu rumfuna a jihar Abia.

Dan takarar na PDP Dauda Lawal ya yi zargin APC na iya yin ta don kawo tarnaki a zaben da ya ke bugun kirji shi ne a kan gaba.

Mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha Gusau, ya musanta hakan da zaiyana cewa an gudanar da zaben cikin adalci kazalika PDP ce ke amfani da jami’ai don neman madafun iko ko a na ha maza ha mata.

Da yawa dai jihohi sun samu sakamakon su, inda duk jihar da gwamnati mai ci ta sha kaye a ka fi samun murna da zolaya.

Zaben 2023 ya fi kowa sauyi a jihohi in an kwatanta da na 2019.Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like