An binne marigayi Sanata Mustapha a makabartar Gabas dake Daura


An binne gawar marigayi sanata Mustapha Bukar, a makabartar Gabas  bayan an yi masa sallar jana’iza a dandalin Kangiwa dake kofar fadar Sarkin Daura, Umar Faruk.

Babban limamin Daura, Liman Salisu Rabi’u, shine ya jagoranci sallar da ta samu halartar gwamna Aminu Bello Masari, mataimakinsa Munnir Yakubu, Ahmad Lawal shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, wanda ya jagoranci sanatoci da dama da kuma yan majalisar wakilai ta tarayya. Sarkin Daura Umar Faruk, tsofaffin ministoci da sanatoci da kuma daruruwan jama’a masu jimami duk sun halarci jana’izar.

An dauki gawar a jirgin sama zuwa Katsina kafin  a dauke ta a  mota  ya zuwa Daura mahaifarsa domin yi masa sallar da aka yi da karfe 5:55 na yamma aka kuma binne shi da karfe 6:10.

A sakonsa na ta’aziya, gwamna Masari ya bayyana damuwarsa kan mutuwar Sanata Mustapha Bukar, Madawakin Daura inda ya bayyana ta a matsayin asara mai ciwo da bakin ciki musamman  ga mutanen Katsina dama Najeriya baki daya.

You may also like