An Birne Mutum Mai Mata 86 A Bidda An binne gawar marigayi Muhammadu Bello Masaba, mutumin nan da yake da mata tamanin da shida wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar asabar.
An binne gawar marigayin ne a jiya Asabar, a mahaifarsa ta Effun Narkodi, cikin garin Bidda.
Shape Nupe, Ndayako da Kpotun Nupe na daga cikin wadanda suka halarci ja’inazar marigayin yayin da mutane suke dakon zuwa gidan marigayin saboda ta’aziyya ga iyalan da ya bari.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like