An Bukaci Majalisun Dokokin Najeriya Su Samar Da Dokar Da Za Ta Magance Matsalar Rushewar Gine-GineANAMBRA, NIGERIA – Mista Alexander Chukwunwike da ke kula da gidauniyar gine-gine ta Najeriya reshen jihar Anambra, ya bayyana wannan bukatar, biyo bayan rushewar wani bene mai hawa biyu da wasu jaridu suka ruwaito cewa ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutum biyu a garin Oraifite da ke karamar hukumar Ekwusigo ta jihar a karshen makon da ya gabata.

Mista Alexander wanda ya ziyarci garin Oraifite don ganema idanunsa yadda lamarin ya faru, ya ce, “mun ga abubuwa da dama a wurin. Na daya, ba mu san ko su waye ne mai ginin ya nada a matsayin kwararru a wurin ginin ba. Amma daga abubuwan da muka gani, akwai wasu abubuwa tattare da yadda ake kula da aikin, saboda mun dubi baraguzan ginin mun ga cewa ba a yi amfani da isasshen kayan aiki ba.

Ya kara da cewa, abu na biyu kuma shi ne, tana yiwuwa ba kwararru ba ne suka gudanar da aikin inda ya ce sun lura an dora wa benen nauyin da ya fi karfinsa saboda bisa ka’ida, ginin bai kamata ya fi hawa guda ba.”

Mista Alexander dai ya dora da yin kira ga manyan majalisun dokoki da su sanya hannu don kirkiro dokar gine-gine ta kasa wato National Building Code, wacce za ta taimaka wajen tace kwararru da kuma magance matsalar rugujewar gine-gine a fadin kasar.

Shi kuwa tsohon ciyaman na kungiyar injiniyoyi ta Najeriya reshen jihar Anambra, Injiniya Edmond Nkalu, ya bukaci hukumomi su yi aikinsu don ganin an bar ayyukan gine-gine a hannun kwararru.

“Abubuwa da yawa na iya kai ga rugujewar gini saboda duk wata tazarar da ba a cike ba na iya rufta gini. Wannan abin damuwa ne sosai, kuma ina fatan hukumomi zasu yi abin da ya kamata. Kuma abin yi shine tabbatar da cewa kwararru ne ke aiwatar da ayyukan gin-gine. Wannan zai rage yawaitar ruftawar benaye.” Nkalu ya ce.

Yanzu rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta ce ‘yan sanda sun ceto wasu mutum biyu daga baraguzan wannan ginin.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Mista Tochukwu Ikenga, “Da muka ji labarin, ma’aikatan mu sun je sun kebe gurin don hana mutane shigowa. Mun ceto mutum biyu daga baraguzan ginin, kuma ana nan ana gudanar da bincike don gano ainihin musabbabin rugujewar ginin.”

Saurari cikakken robots daga Alphonsus Okoroigwe:

You may also like