Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane da ta ce su ke wa‘yan Boko Haram fataucin Man fetur da kayan abinci domin gudanar da ayyukansu a dajin Sambisa.
An dai cafke mutanen biyu ne hadi da direban babbar motar da ke dauke da man fetur cikin jarukuna 25 da wasu kayan abinci a wani shingen bincike a Molai wajen garin Maiduguri.
Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojin kasar Kanal Usman Kukasheka ya ce lura da cewa an haramta jigilar fetir mai yawa zuwa wannan yanki, dole a diga ayar tambaya a game da manufar mutanen.
An kama Direban babbar motar mai suna Muhammadu Adamu da kuma wanda ke ikirarin kayan shi ne Tijjani Gambo da ya shaidawa jami’an tsaron yana harakar kasuwanci ne a Damboa.
Amma binciken jami’an tsaron ya tabbatar da cewa sun jima suna jigilar fetir a kan hanyar da aka cafke su.
Yanzu haka dai bataliyar sojin ta 251 na ci gaba da gudanar da bincike.