An Cafke Wasu ‘Yan Boko Haram A Wani Kauyen Jihar Zamfara 



Rundunar Sojin Najeriya dake Gusau a Jihar Zamfara sun bada sanarwar cafke wasu mutane 3 da ake zargin yan Boko Haram ne a Mashema dake karamar hukumar mulkin Zurmi.
Kwamandan Rundunar, Kwanel Abdullahi Adamu wanda ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yace yan banga ne sukayi nasarar cafke mutanen, kana suka mika su ga masarautarta Zurmi
Kanel Adamu yace cikin makaman da aka kamasu dasu sun hada da bindiga kirar AK 47 da harsashe 600 da kuma kwayoyi da layu a tare da wadanda aka kaman
Ya kara da cewa tuni aka mika su ga hukumomin Soji dake Kaduna domin ci gaba da bincike

You may also like