
Asalin hoton, Getty Images
Mahukuntan Premier League sun canja ranar da ya kamata a fafata a wasan Premier League tsakanin Arsenal da Chelsea.
‘Yan sanda ne suka bukaci hakan, domin samar da matakan tsaro da kula da lafiyar magoya baya a ranar buga wasan na hamayya.
Gunners tana matakin farko a teburin Premier da tazarar maki shida tsakani da Manchester City ta biyu, mai kwantan wasa daya.
Arsenal da City za su kara a Etihad a wasa na biyu a Premier League ranar 26 ga watan Afirilu – daga nan Gunners ta fuskanci Chelsea kwana uku tsakani.
To sai dai Premier ta sanar da dage karawar da ya kamata a yi tsakanin Arsenal da Chelsea zuwa ranar Talata 2 ga watan Mayu, kamar yadda ‘yan sanda suka bukata.
Chelsea wadda take ta 11 a Premier League za ta fafata da Real Madrid ranar Laraba a wasan farko a zagayen quarter finals a Champions League.
Chelsea wadda ba ta yin kokari a kakar bana ta sake nada Frank Lampard kociyan rikon kwarya, bayan da ta sallami Graham Potter.
Arsenal na fatan daukar Premier League a karon farko tun bayan 2003/04 karkashin Arsene Wenger.