
Asalin hoton, AFP
Likita ya ce jaririyar na samun sauki
Masu aikin ceto sun zakulo wata jaririya daga karkashin buraguzan wani gini a arewa maso yammacin Syria, yankin da girgizar-kasa ta yi wa mummunan barna.
Wani dan uwan iyayen jaririyar ya ce mahaifiyar jaririyar tana kan nakuda a lokacin da girgizar ta faru, inda kuma ta haihu kafin ta rasu.
Haka nan mahaifin jaririyar da sauran ‘yan uwanta hudu duk sun rasu sanadiyyar girgizar-kasar.
Wani bidiyo ya nuna yadda wani mutum ya dauko jinjirar turbude da kura bayan an zakulo ta daga karkashin buraguzan gini a garin Jindayris.
Wani likita a asibitin da ke makwaftaka ya ce a yanzu jaririyar ta samu sauki.
Gidan da iyalan jaririyar suka kasance na daga cikin gidaje 50 wadanda girgizar kasar ta lalata a Jindayris, wanda ke kan iyakar Syria da Turkiyya.
Kawun jaririyar, Khalil al-Suwadi ya ce ‘yan uwa sun garzaya a lokacin da suka lura da ruftawar gidan.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa “mun ji kara a lokacin da muke kokarin kawar da buraguzai, sai muka kwashe turbayar muka ga jaririya da cibiyarta a hade da ta mahaifiyarta, sai muka yanke cibiyar sannan dan uwana ya kai ta asibiti.”
Likitan yara mai suna Hani Maarouf ya ce an kawo jaririyar asibiti cikin mummunan yanayi “jikinta duk ya gurje.”
“Haka nan lokacin da aka kawo ta yanayin dumin jikinta ya yi kasa saboda sanyi. Dole sai da muka dumama jikinta kuma muka ba ta magani.”
An dauki hoton jinjirar tana kwance cikin kwalba kuma an sa mata ruwa, daidai lokacin da a bangare daya ake yi wa mahaifiyarta, Afraa, da mahaifinta, Abdullah, da kuma sauran yan uwanta hudu jana’iza.
Suna daga cikin kimanin mutun 2,000 da girgizar-kasa ta hallaka a Syria, kamar yadda alkaluma suka nuna.
A Turkiyya ma dubban mutane ne girgizar ta yi sanadin rayukansu.