An ceto wasu ‘yan ci rani a girka


Sojoji masu tsaron gabar ruwa a Girka sun ce sun ceto ‘yan gudun hijira fiye da 300 cikin kogin Agean.An ceto mutanen kwanaki tara da suka wuce, yayin da kuma sojojin na Girka suka ce sun sami nasarar ceto wasu ‘yan gudun hijirar 59 a kusa da tsibirin Kos. 
Hakan nan kuma sojojin sun kama wasu mutum biyu masu safarar mutane tare da kwace jiragen ruwa guda 4. Galibin jiragen ruwan da ake safarar mutanen jirage ne marasa inganci inda kuma a yawancin lokuta su kan kife da mutane.

You may also like