An ceto yan Najeriya 1,317 a cikin kwanaki 10 daga ƙasar Libya


Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce jumullar yan Najeriya 1317 suka dawo gida dan kashin kansu cikin kwanaki goma da suka wuce bayan da suka makale a ƙasar Libya da yaƙi ya daidaita a ƙoƙarin da suke na ƙetarawa zuwa nahiyar Turai.

Shugaban hukumar ta NEMA, Mustapha Maihaja shine ya bayyana haka yayin da yake karɓar karin wasu yan Najeriya 116 da suka iso kasarnan da safiyar ranar juma’a.

Sababbin rukunin mutanen da suka dawo sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos, cikin wani jirgi mallakin kamfanin jiragen sama na  Buraq da karfe 5:39 na asuba.

A ƙalla yan Najeriya 3000 ne suka dawo daga ƙasar ta Libiya ta hanyar wani shiri na hukumar dake kula da yan ci rani ta duniya, a cikin yan watannin da suka gabata.
Maihaja wanda ya samu wakilcin Sulaiman Yakubu, jami’in da ke lura da aiyukan hukumar a yankin kudu maso yamma yace yan Najeriyar sun dawo gidane cikin rukuni daban-daban tsakanin ranakun 5 zuwa 15 ga watan Disamba da taimakon kungiyar tarayyar Turai.

Maihaja ya ce gwamnatin tarayya zata ci-gaba da  hada kai da ƙungiyar domin ganin an kwaso ragowar yan Najeriya dake Libya inda  suke fuskantar wahalhalu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like