A kalla Falasdinawa 16 ne suka ji rauni a wani tashin hankali da aka yi a Yammacin Kogin Jordan, yayin da ake zanga-zangar nuna adawa da matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da Kudus babban birnin Isra’ila.
Rahotanni sun nuna cewa mutane sun samu raunukan ne sakamkon jefa musu hayaki mai sa hawaye da harsashin roba, amma an ji wa mutum daya rauni sakamakon harbinsa da aka yi da harsashi.
Isra’ila ta girke karin daruruwan dakaru a Yammacin Kogin Jordan.
Sanarwar da Mista Trump ya yi dai ba ta samu karbuwa ba a duniya baki daya, inda ake yin tur da hakan saboda sauya tsarin Amurka na gomman shekaru a kan wannan lamari mai sarkakiya. Falasdinawa mazauna Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza sun mamaye tituna don gudanar da zanga-zanga.