Wata kungiyar kare hakkin bil-adama a kasar Turkiyya mai suna ‘Turkey’s Human Rights Association (İHD)’ da ke a lardin Diyarbakır ta fito da wani rahoto ranar Litinin din nan cewa shekarar 2016 ta kasance tamkar annoba a kasar game da tauye hakkin dan adam tun daga shekaru 500 da suka gabata,
musamman lokacin da gwamnatin kasar karkashin Mai Girma Shugaban Kasar
Recep Erdogan ta kakaba dokar ta-vaci jim kadan bayan yunkurin juyin mulkin
da bai yi nasara ba a ranar 5 ga Yulin bara.
Rahoton ya kara da cewa kimamin ‘yan jarida 131 aka kulle yayin samamen da
ake kaiwa da niyyar hamvarewa gami da gurfanar da dukkan masu hannu a cikin
yunkurin na juyin mulkin. Rahoton har ila yau, ya bayyana cikin wadanda irin wannan samamen ya rutsa da su, har da da malaman makaranta da ‘yan kasuwa, wadanda a shekarun baya suka gabatar da korafinsu kan Shugaba Erdogan na kasar, bayan furucin da ya yi a kasar a watan Fabrairun 2014, inda ya lashi takobin shiga lungu da sako na tasa kyeyar mabiya Gulen a ko’ina suke a cikin kasar.
Sai dai akwai alamun da biyu a ke dukan biri da rani a cikin kasar ta Turkiyya, wato tun daga fushin damina! Manyan tambayoyin da al’ummar duniya suka kasa fahimta ya zuwa yau shi ne, mene ne dalilin da ya sanya ake yakar bangare daya kawai? Me ya sa hukumomin kasar ta Turkiyya suka dora karar-tsana a kan fitaccen Malamin kasar, Fethullah Gulen? Wasu daga cikin rahotannin na cikin gida sun tabbatar da cewa rikicin tsakanin Shugaba Erdogan da Sheikh Gulen ba ya rasa nasaba da siyasa. A cewar rahotannin, Gulen yana daga cikin fitattun mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ba wa Shugaba Erdogan goyon bayan samun shiga gidan sarautar kasar, amma daga bisani, wasu ‘yan ba-ni-na-iya suka shiga tsakani, wanda hakan ta tilasta wa Sheikh Fethullah barin kasar tasa ta gado, ya koma cikin kasar Amurka, inda a yanzu yake zaman gudun hijira.
Fethullah dai, kamar yadda rahotanni daga kafafen yada labarai na duniya suke nuni fitaccen malami ne da ya shafi shekaru da dama yana yin kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da tafarkin rayuwar fiyayyen halittu Annabi Muhammad (SAW). Muhimmin sakonnin yake aikawa a ko’ina a duniya shi ne, Musulmi shi ne kadai tsayayyen mutumin da zai iya tabbatar da zaman lafiya a doron kasa, ta hanyar ayyuka nagari, yin riko da sunnonin Manzo
(SAW). A mafi yawan rubuce-rubucensa, Sheikh Gulen ya fi mayar da hankali
kan yadda ake vata sunan addinin Musulunci musamman a yanzu da duniya ke kokarin danganta wasu gungiyoyin ta’addanci da Islam. A mafi yawan ra’ayoyin malamin, yana koyar da tsantsan zama a matsayin masu neman ilmi da aiki da shi.
An dai ce malamin kusan ya fi kowa magoya baya daga ‘yan kasarsa, a ciki da wajen kasar ta Turkiyya, wanda a halin yanzu ya bude cibiyoyin koyar da ilmin addinin Islama a Nahiyoyi da dama, ciki, har da Afrika da mafi yawan kasashen na kasashen na Afrika, har ma da Nijeriya a ciki. Baya ga wannan ya kasance a kan gaba wajen yada manufar addini ta hanyar rubuce-rubucen
littattafan da a yau ake fassara su zuwa yaruka sama da 60 na Afrika.
Faruwar yunkurin juyin mulkin nan, Sheikh Gulen yana da cikin sahun gaba na wadanda suka fito suka soki lamirin yunkurin da sojoji suka nemi a Turkiyya. Kana kuma ya yi kira da babbar murya ga hukumomin kasar tasa da su gaggauta gudanar da binciken gano wadanda suke hannu a cikin a bin da ya
fassara da bakar aniyarsu. Ya kara da cewa a daidai lokacin da duniya ke ci gaba da kurvar madarar dimokuradiyya, bai ga amfanin sojoji marasa kishin kasa ba, da har za su fito suna kokarin maida kasar baya ba.
Jim kadan bayan dukkanin sakonnin nan da Sheikh Gulen yake aikewa zuwa ga
mahukunta kasar tasa ta Turkiyya, sai ga shi a rana tsaka kallo ya nemi komawa sama, a lokacin da Shugaban Kasar Recep Erdogan ya bayyana Sheikh Gulen da cibiyarsa ta ‘Hizmet’ a matsayin daya daga cikin wadanda suka shirya yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Jin haka, kamar yadda na karanta a wasu daga cikin manyan jaridun kasashen Turai da Amurka, Sheikh Gulen ya fito ya karyata zancen na Shugaba Erdogan. Kana kuma ya kara jaddada manufarsa, sannan ya nesanta kansa da cibiyarsa ta Hizmet daga abin da shugaban na Turkiyya ya bayyana.
Dukkanin kiraye-kirayen da Shehin malamin yake yi, rahotannin ciki da wajen kasar sun kara bayyana matakin da gwamnatin kasar ta dauka, inda suke kara tsaurara matakai ga dukkanin wanda suka fahimci yana da wata alaka da shehin malamin ko cibiyoyin na karatu.
Kan hakan ne gwamnatin Erdogan take sanya takunkumi daban-daban a kan ‘yan
jarida, inda gwamnati ta sa aka kulle akalla gidajen jaridu sama da dubu dari biyar a cikin kasar. Ba wannan kadai ba, gwamnati ta bayar da umarnin kame duk wani dan jaridar da aka lura yana neman zama barazana ga irin wadannan muradun da Erdogan. Haka kuma ya zuwa yanzu milyoyin mutane na can suna hutawa a cikin gidajen yari daban-daban na kasar.
A gefe guda kuma, tun daga lokacin da Shugaba Erdogan ya bayyana gudurinsa
na farautar dukkan masu hannu a cikin yunkurin na juyin mulki da bai yi nasara ba, ya aike wa gwamnatin kasar Amurka da ta gaggauta dawo musu da Sheihin malamin zuwa kasarsu domin fuskantar kalubalen da ke gabansu. Haka ma, ya rika aikewa da manzanni ko’ina a cikin kasashen Afrika, inda ake gudanar da harkokin cibiyar fitaccen malamin, ciki, har da Nijeriya.
A Nijeriya dai, yayin da Ambasadan kasar ta Turkiyya ya gabatar da kudurin ga gwamnati, hukumomi sun mayar wa gwamnatin kasar martanin cewa babu wata
gwamnati da za ta zo cikin Nijeriya ta nemi ta yi amfani da ita wajen cimma wani buri nata na siyasa. Gwamnatin ta Nijeriya ta kara da cewa.