
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi rashin nasara a gida a hannun Villareal a wasan mako na 28 a La Liga ranar Asabar, karo na biyar da aka doke ta a bana.
Villareal ta ci Real 3-2 a Santiago Bernabeu, kuma Samuel Chukwueze ne ya ci na uku da ya bai wa baki maki ukun da suke bukata.
Wasa na uku kenan da suka fafata a tsakaninsu a kakar nan, inda Villareal ta ci Real gida da waje a La Liga, Real ta fitar da Villareal a Copa del Rey.
Wasa uku da suka kara a bana:
La Liga Asabar 8 ga watan Afirilu
- Real Madrid 2 – 3 Villarreal
Copa del Rey 19 ga watan Janairu
- Villarreal 2 – 3 Real Madrid
La Liga Asabar 7 ga watan Janairu
- Villarreal 2 – 1 Real Madrid
Karo na biyar da aka ci Real Madrid a La Liga a bana:
Litinin 7 ga watan Nuwambar 2022
- Rayo Vallecano 3 – 2 Real Madrid
Asabar 7 ga watan Janairun 2023
- Villarreal 2 – 1 Real Madrid
Lahadi 5 ga watan Fabrairun 2023
- Mallorca 1 – 0 Real Madrid
Lahadi 19 ga watan Maris din 2023
- Barcelona 2 – 1 Real Madrid
Asabar 8 ga watan Afirilun 2023
- Real Madrid 2 – 3 Villarreal
Da wannan sakamakon Real tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya.
Ita kuwa Villareal ta yi sama zuwa mataki na biyar da tazarar maki hudu tsakaninta da ta hudun teburin gurbin Champions League.
Watakila Barcelona ta kara bai wa Real tazarar maki 15 idan ta doke Girona ranar Litinin a La Liga fafatawar mako na 28.
Ranar Laraba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan farko a quarter finals a Champions League.
Daga nan Real za ta je gidan Cadiz a wasan mako na 29 a La Liga ranar 15 ga watan Afirilun 2023.