An Ci Tarar Wasu Dillalan Mai Bilyan 2.5 Kan Karkatar da Lita Milyan 9 Na Fetur


Hukumar Albarkatun Man Fetur Ta Kasa( DPR) ta ci tarar wasu dillalan mai Naira Bilyan biyu da rabi bisa laifin karkatar da lita milyan tara na fetur.

Da yake karin haske kan matakin, Kakakin Hukumar Sa’idu Bulama ya ce, dalilin da ya sa tun da farko ba a gano wannan Almundahanar shi ne saboda fetur din da aka ba su yana daga cikin rukunin gaggawa ne da kamfanin NNPC ya samar a watan Disamba don rage matsalar karancin fetur da aka fuskanta.

You may also like