An Cika Shekaru Sace Dalibai Mata 276 Daga Makarantar Sakandare Ta ChibokABUJA, NIGERIA – Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da wajen kasar, amma har yanzu gwamnati tana cewa ta damu, to sai dai wadanda abin ya shafa sun ce akwai alamar gazawa.

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

Wananna lamari na sace ‘yan matan ya faru ne a ranar 14 ga watan Afrilu ta shekara 2014, kuma tun lokacin ake ta ce-ce-ku-ce akan lamarin.

A Najeriya, tsohuwar ministar Ilimi Oby Ezekwesili, da tsohuwar babban darekta na hukumar tashoshin ruwa ta Najeriya, Hadiza Bala Usman da wata ‘yar fafutukar kwato wa mata ‘yanci Aisha Yesufu sun kwashe shekaru hudu suna gudanar da zangazanga a karkashin maudu’in “Bring Back Our Girls” domin matsa wa gwamnati lamba ta kwato ‘yan matan.

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

Wani abu da uwargidan shugaban kasar Amurka a lokacin, Michelle Obama ta bi sahun kasashen duniya na neman a dawo da ‘yan matan.

Gwamnatin Shugaba Mohammadu Buhari ta samo wasu da dama daga cikin ‘yan matan amma har ya zuwa yau, akwai sauran 98 wadanda ba a san inda suke ba.

Taron Tuna 'Yan Matan Chibok A Washington, D.C.

Taron Tuna ‘Yan Matan Chibok A Washington, D.C.

A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban ‘yan asalin Chibok mazauna birnin tarayyya Abuja, Nkeki Mutah ya yi bayani cewa, wannan abu yana damun su har yanzu, ganin cewa wasu iyayen ‘yan matan dayawa sun kwanta dama a sanadiyar bacewar ‘ya’yan nasu.

Nkeki ya ce duk alkawuran da gwamnati ta yi masu na cewa za ta jajirce ta ga an dawo da ‘yan matan, bai yi kai ba kuma bai yiwu ba har yanzu. Nkeki ya ce daga baya ma an sace wasu ‘yan matan daga Dapchi na kasar Yobe, a can ma har yanzu akwai Leah Sharibu da har yau babu labarin ta.

NEJA: Addu'ar a sako 'yan matan Chibok da Dapchi

NEJA: Addu’ar a sako ‘yan matan Chibok da Dapchi

Nkeki ya ce tunda akwai sauran makonni kafin wannan gwamnatin ta bar gadon mulki, suna rokon a taimaka masu ko Allah zai sa a dace da samo ‘yan matan.

A baya, Ministan Sharia Abubakar Malami ya fito ya ba iyayen da kungiyoyi karfin gwiwa cewa gwamnati tana iya kokarin ta na ganin a kwato ‘yan matan daga hannun wadanda suka sace su. Malami ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba, duk da cewa ba ta samu nasarar kwato ‘yan matan duka ba.

Ita kuwa tsohuwar Ministar Ilimi Oby Ezekwesili da ta jagoranci zangazangar a baya, ta amince cewa akwai gazawar gwamnati a lamarin, wani abu da daya daga cikin jiga-jigan fafutukar, Aisha Yesufu ta yi tsokaci akai a wannan lokacin cewa akwai lauje cikin nadi.

Cikar 'Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram

Cikar ‘Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram

Aisha ta ce gwamnati ba ta samo makamai ba, saboda haka mayaka ba su iya yin aikin kwato ‘yan matan ba. Aisha ta ce ya kamata a gano wadanda ba su yi aiki yadda ya dace ba a hukunta su.

Wasu cikin ‘yan matan sun samu tallafin karatu har kasar Amurka, inda a watan Mayu na bara, Lydia Pogu ta samu digirin-digigir a fannin gudanar da ayyukan ‘Dan Adam daga Jami’ar kudu Maso gabashin kasar Amurka, hakan ya zo ne bayan ta kammala digirin farko a fannin Shari’a da Kimiyar Siyasa.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like