Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya cire Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal daga shugabancin kwamitin da ke tace sunayen wadanda za a nada shugabannin gudanarwar hukumomin gwamnatin tarayya inda aka maye gurbinsa da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta nuna cewa Shugaban ya dauki matakin ne bayan koke koken da ake ta gabatarwa kan yadda Sakataren gwamnatin ke tafiyar da ayyukan kwamitin inda Buhari ya nemi shugabannin majalisar tarayya da Shugaban kungiyar gwamnoni kan su shiga cikin kwamitin don taimaka wa wajen zakulo wadanda suka cancanta.
‘Ya’yan kwamitin dai sun hada da Alhaji Mai Mala Buni (wakilin Arewa maso Gabas), Alhaji Zakari Ede (wakilin Arewa ta Tsakiya), Alhaji Inuwa Abdulkadir (Arewa maso Yamma), Chief Hillard Etagbo Eta (kudu maso kudu), Chief Pius Akinyelure (kudu maso Yamma), Chief Emmanuel Eneukwe (kudu maso Gabas ) sai Mr. Gideon Sammani, a matsayin Sakataren kwamitin.