An cire bankin UBA daga haramcin Hada-Hadar waje. 


Babban bankin Najeriya, CBN, ya cike bankin UBA daga cikin jerin bankunan da ya hana su hada-hadar kudaden waje, saboda bankin ya mika kudaden NNPC dake hannunsa.Wata sanarwar da CBN ta fitar ta ce dage haramcin a kan bankin na UBA zai fara aiki ne a ranar Alhamis.
Tun da fari dai CBN ta hana bankuna tara yin dukkan hada-hadar da ta shafi amfani da kudaden kasashen waje, har sai sun mika kudaden asusun kamfanin mai nakasar, NNPC da ke hannusu zuwa asusun bai daya na gwamnatin tarayya.

Masu sharhi a kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan matakin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like