‘Yan majalisar wakilai ta kasa sun cire sunan Jihohin Kano da Filato daga cikin jerin wadanda za su amfana da hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas, a wani zaman majalisar da Sanata Ali Ndume ya jagoranta.
Idan ba a manta ba, sanya sunan Jihohin ya janyo cece-kuce daga bangarori daban-daban.
Tun Farko An saka sunayen jihohin ne ganin cewa suma sun fada komar tashe tashen hankula fiye da wasu jihohin da suke arewa maso gabashin kasar nan.
Idan muka Dauki jihar kano kadai ta ishemu misali , ganim adadin mutanen da suka rasa ransu ta hanyar rikicim ‘yan Tada kayar baya a shekarun baya, jihar Filato ma sum fuskanci irin wannan matsala.
Shirin anyi shi don amfanar da jihohin da suka fuskanci wadannan matsaloli na ‘ yan tada kayar baya.