An dakatar da Lewandowski wasa uku a jere a La Liga



An bai wa Lewandowski katin gargadi sau biyu a wasan da suka yi nasara a kan Osasuna da ci 2-1

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An bai wa Lewandowski katin gargadi sau biyu a wasan da suka yi nasara a kan Osasuna da ci 2-1

Kotun wasanni ta Sifaniya ta hukunta dan wasan gaban Barcelona Robert Lewandowski ta hanyar dakatar da shi wasanni uku a jere.

An bai wa Lewandowski jan kati a wasan da Barcelona ta yi da Osasuna gabanin tafiya hutun kofin duniya da aka fara a watan Nuwamba.

Wata kotu a Madrid ce ta dakatar da hukuncin da aka yi masa a makon jiya, wanda hakan ya bai wa dan wasan damar buga wasan da suka yi canjaras da Espanyol 1-1 a ranar Asabar.

Yanzu dai dan kasar Poland din mai shekara 34 ba zai buga wasan da Barcelona za ta yi ba da Atletico Madrid da Getafe da kuma Girona.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like