
Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da rafli, Fernando Hernandez a Mexico wasa 12, bayan da ya yi wa dan wasa gula da gwiwar kafarsa a matsaimatsi.
Lamarain ya faru ne ranar Lahadi a fafatawa tsakanin America da Leon.
Hernandez ya yi wa dan kwallon Leon, Lucas Romero gula a lokacin da cikin fushi tare da takwaransa suka bukaci raflin ya je ya duba VAR, bayan da America ta farke kwallo 2-2.
Shi kansa dan wasa Romero, wanda aka yi wa gula a matsaimatsin, an dakatar da shi wasa biyu.
”Ina neman afuwa daga ‘yan kallo da masu bibiyar tamaula da Romero kan abin da na aikata,” in ji koci Hernandez.
”Ba zan kara aikata laifi irin wannan ba, na san doka, zan kuma bi hukuncin da aka zartar a kaina.”
Bayan tashi daga karawar Hernandez ya ce bai daga murya sai an hukunta Hernandez ba, domin rashin jituwa suka samu.
”Rafli mutane ne dole suma za su iya yin kuskure, abin da ya fara rashin jituwa ne kawai tsakanin mu,” kamar yadda ya sanar da kafar yada labarai TUDN.
Leon da America suna mataki na uku da na hudu a teburin babbar gasar tamaula ta Mexico a bana.
Wasan da suka kara na hamayya ranar Lahadi, an kori kociyoyin kungiyoyin wato Fernando Ortiz da Nicolas Larcamon.
An yi ta yawo da hoton kociyan Leon, Larcamon a kafar sada zumunta an yamutsa masa rigarsa, sakamakon fada da ya yi da yan bencin America.
Dukkan kociyoyin kungiyoyin an dakatar da su wasa bibiyu.