An dakatar da ‘yan sanda 8,000 a Turkiyya


Hukumomi a Turkiyya sun dakatar da ‘yan sanda 8,000, wadanda rahotanni suka ce suna da alaka da yunkurin juyin mulkin da aka yi a karshen mako.

Tuni aka tsare sojoji da ma’aikatan shari’a 6,000, ciki harda manyan janar-janar.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin kawar da “gubar” da ya ce ita ce ta haddasa boren.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry, ya nanata bukatar bin tsarin demokuradiyya.

Da ya ke magana a birnin Brussels inda ya ke tattaunawa da ministocin harkokin wajen Turai, Mr Kerry ya ce Amurka na goyon bayan zababbiyar gwamnatin Turkiyya.

“Hakika muna goyon bayan ladaftar da wadanda suka shirya juyin mulkin, amma kada a wuce gona-da-iri”.

Gwamnatin Turkiyya ta zargi malamin addini Fethullah Gulen da shirya kifar da gwamnatin.

Mista Gulen wanda ke zaune a Amurka ya musanta hannu a lamarin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like