An dakile shirin kai harin ta’addanci a wasannin Olympics


Jami’an tsaro sama da 80,000 ne zasu kasance cikin sintiri a fadin birnin Rio a yayin wasannin Olympics.

Yan sanda sun kama wasu mutane 10 bisa zarginsu da kitsa kai hare-haren ta’addanci a lokacin wasannin Olmpics da ya rage makwanni biyu a fara a birnin Rio.

Kodayake hukumar yan’sandan kasar Brazil tace mutanen goma ba ‘yan kungiyar ISIL bane sai dai tabbas wadanda ake zargin sunyi kokarin tuntubar kungiyar bisa niyyarsu.

Ministan shari’ah na kasar Brazil Alexandre Moraes ya ce dukkaninsu ‘yan asalin kasar Brazil ne kuma suna tsaka da shirya awaitar da hare haren yayin gasar ta Olympics kafin a cafke su.

Jami’an tsaro sunce tun da farko dai gungun mutanen sun yi kokarin siyan bindigogi kirar AK47 daga wajen wani mai safarar makamai dake kasar Portugal sai dai babu cikakkakiyar shaidar hakan.

Lamarin yasa gwamnatin kasar Brazil kiran taron gaggawa don tattauna yadda za’a bullowa barazanar tsaron musanman a yayin wasanin Olympics.

Ana dai sa ran cewa sama da yansanda da sojoji dubu tamanin ne zasu kasance cikin sintiri a fadin birnin Rio a yayin gudanar da gasar ta Olympics har zuwa rana karshe wato 21 ga watan Agusta mai zuwa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like