An Daure Wasu jakuna 8 A Gidan Kurkuku A kasar Indiya an daure wasu jakuna har tsawon kwanaki 4 sakamakon yadda suka ka yi kiwo da cin abinci a iyakar wani gidan kurkuku. 

Labaran da tashar New Delhi TV ta bayar na cewa lamarin ya faru ne a gundumar Jalaun da ke jihar Uttar Pradesh bayan da jakunan 8 suka ci ciyayin da ke kurkukun sakamakon haka mahukuntansa suka daure su har na kwanaki 4. 

Wani jami’in gidan kurkukun R K Mishra ya bayyana cewa jakunan sunyi barna ga wasu shuke-shuken gidan kurkukun da ke lambunsa. A baya an gargadi masu jakunan da su daina barinsu suna zuwa kusa da kurkukun amma ba su jiba, 

Sakamakon haka aka kama jakunan tare da kullesu amma an saki jakunan ne bayan da wani dan siyasar yankin ya biya kudin barnar da suka yi.

You may also like