An dawo da Alqaryar fina-finai a Jihar Kano. 


Sanusi-Lamido-Sanusi-1

 

 

Mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusina II ya mayar da martani kan dambarwar soke alkaryar fina-finai a Kano da gwamnatin tarayya ta yi cikin watan jiya. 
Sarkin ya kuma yi kira ga hukumomi su sake tunani a kan matakin da suka dauka.Ya kuma nemi a zauna da malamai domin tantance hanyar da za a rage illar da za a iya samu sakamakon kafa alkaryar fina-finan, tare da futo da hanyar anfana da ita yadda ya kamata.

Mai martaba Sanusi ya kara da cewa ba dai-dai ba ne dauke alkaryar fina-finan daga Kano wadda ta yi fice kan harkar shirya fina-finan Hausa.Sarki Sanusi II ya kuma bayyana cewa idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata za a iya samar da fina-finan da za su amfanar da al’ummar Hausawa, musamman wadanda za su fito da tarihin shugabannin addini, kamar su Shaikh Usmanu Dan Fodiyo.

Sarkin dai ya na bayani ne lokacin da ayarin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano suka kai ziyara fadarsa.

You may also like