An fadada neman yan matan Dapchi ya zuwa makotan kasashen Nijar,Chadi da Kamaru


Gwamnatin tarayya ta ce ta fadada neman yan matan makarantar sakandaren Kimiyya da Fasaha dake Dapchi, a jihar Yobe da  yan Boko Haram suka sa ce, ya zuwa makotan kasashen Nijar,Kamaru da Chadi.

Lai Muhammad, ministan ya da labarai shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Muhammad ya ce manyan shugabannin tsaro sun tafi ya zuwa yankin arewa maso gabas a ranar Alhamis domin su kara taimakawa wajen binciken da yanzu aka fadada shi fiye da yankin arewa maso gabas.

Cikin manyan jami’an tsaron da suka tafi ya zuwa yankin sun hada da, Gabriel Olanisakin Babban hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai shugaban rundunar sojin Najeriya, Ibok-Ete Ekwe Ibas, shugaban rundunar sojin ruwa da kuma Lawal Daura shugaban hukumar tsaro ta farin kaya.

Za su haɗu da shugaban rundunar sojin sama Saddique Abubakar wanda tun da farko ya koma ya zuwa yankin da kuma mai bawa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno.

You may also like