An fallasa yadda cuwa-cuwar neman aiki ke yawaita a Indiya



A baya an sha yin zanga-zanga a Indiya kan satar jarrabawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya an sha yin zanga-zanga a Indiya kan satar jarabawa

Da sanyin safiyar wata rana a watan Disamba, ‘yan sanda a Gabashin Jihar Rajasthan suka ga wata motar bas ta nufi yankin birnin Udaipur, sai suka bi ta a baya.

A daren ranar, an kwarmata musu labarin za a fitar da tambayoyin jarabawar daukar malamai na makarantun gwamnatin jihar ta bayan fage kafin miliyoyin mutane su zauna domin rubuta jarabawar.

An sanya cibiyoyi 1,193 domin rubuta jarabawar, wadda aka dade ana tsimayi a ranar 24 da Disamban.

A kasar Indiya, inda ake rububin neman aikin gwamnati, labarin bin bayan fage wajen neman aikin ba sabon abu ba ne.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like