An Fara Barazanar Korar Musulmi Daga Amurka



Kungiyar Musulman Amurka ta ce an aike da wasu gajerun wasiku dauke da sakonni iri daya zuwa wasu masallatai a California tare da yiwa Musulmai munanan kalamai inda aka shaida musu cewa su tattara inasu-inasu su bar kasar.
Sakon ya kuma jinjina wa zababben shugaban kasar Donald Trump tare da bayyana cewa zai tsarkake Amurka. Majalisar kula da danganta tsakanin Musulman Amurka ta bukaci jami’an ‘yan sanda da su gudanar da bincike kan abun da ta kira barazana ta fuskar addini. A lokacin yakin neman zaben sa dai Mr Trump ya sha alwashin haramtawa Musulmai shiga Amurka saboda zargin alakanta wasu kungiyoyin Musulmai da ta’addanci.

You may also like