An Fara Bayyana Damuwa Game Da Shinkafar KebbiWani shugaban kungiyar manoman shinkafa a jihar Kebbi Alhaji Sahabi Augie ya bayyana damuwarsa game da yadda wasu jihohi da kasashen waje ke rubibin zuwa sayen shinkafar da aka noma a jihar Kebbi wacce aka sarrafa ta a jihar Legas tare da kaddamar da ita cikin makon da ya gabata karkashin sunan LAKE RICE. 
Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali wajen sayen wannan shinkafa da tara ta a wani rumbu na musamman, domin kaucewa karewar shinkafar a Arewa da Nijeriya baki daya, saboda ingancin ta. 

You may also like