An Fara Biyan Bashin Kudin Tallafin Karatu(Scholarship)  A Jihar JigawaRahotanin daga Jihar Jigawa, na nuni da cewa tuni gwamnatin Jihar Jigawa ta fara biyan dalibai ‘yan asalin Jihar kudadensu na tallafin karatu wato scholarship, duk da cewa tsohowar gwamnatin da ta shude ne ta tafi da bashin kudaden nasu. 
Rabon dai da a biya dalibai wannan kudin tun shekarar 2014, sai dai kuma yanzu ana biya daliban ne tare da bashin da suke bi, wato bayan an biya tsohon bashin, sai kuma a kara dora sabon tallafin a sama, duk da bincike ya nuna cewa  tuni wasu daga cikin daliban suka kammala karatukansu. 
A makon da ya wuce ne dai Gwamnan Jihar Jigawa  ya bada umarnin a biya dukkan daliban na Jihar Jigawa hakkinsu.

You may also like