Ma’aikatan kiwon lafiya a Najeriya sun fara rigakafin cutar sankarau a wani yunkurin na dakatar da cu gaba da yaduwar cutar bayan Sama da mutum 300 sun rasa rayukansu sakamakon annobar tun a bara.
Ma’aikatan na mayar da hankulansu kan jihar Zamfara da ke arewa-maso gabashin kasar, inda nan ce cibiyar barkewar annobar. Cibiyar shawo kan cututtuka ta Najeriya ta ce za a yi rigakafi ga mutum 500,000. Jami’an kiwon lafiya sun ce akwai kusan mutum 3,000 wadanda ake zaton suna fama da annobar sankarau.
A bangare daya kuma, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi ya yi raddi ga ikirarin Gwamnan Jihar Zamfara, AbdulAzizi Yari wanda ya alakanta cuyar da sabon Allah inda Sarkin ya nuna cewa wadannan kalaman kuskure ne inda ya kalubalanci Gwamnan kan ya fito fili ya shaidawa mutanensa cewa bai mallaki maganin cutar ba a maimakon irin wannan ikirarin.