Hukumar kula da inganci magunguna da kayayyakin abinci a Nijeriya NAFDAC ta gargadi mutane game da wani rahoto da ta samu da ke nuna cewa an shigo da gari Nijeriya daga kasar Indiya.
Yayin da ta ke ci gaba da bincike akan al’amarin, hukumar ta gargadi ‘yan Nijeriya da su guji saye ko kuma cin garin domin kuwa ba ta tantance ko garin ya na da wani hatsari ga lafiya ba.
Daraktar hukumar Misis Yetunde Oni ita ta isar da wannan sako a wani taron wayar da kan jama’a game da ayyukan hukumar da aka yi a garin Illorin, inda ta ce binciken su na farko ya gano cewa garin an yi shi ne a kasar Ghana, an kuma kunshe shi a kasar Britaniya, ba kasar Indiya ba kamar yadda suka samu rahoto da farko.
Haka shi ma ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole ya bayyana a shafin sa na Twitter cewa yanzu haka hukumar ta NAFDAC ta kwace kunshin garin guda 26 wadanda ta samu a wani babban shagon sayar da kayayyakin masarufi a Ikoyi da ke jahar Lagos