An Fara Shirin YiWa Wani Sanatan Kaduna Ta Arewa Kiranye Daga Majalissa Al’ummar Kaduna Ta Arewa Sun fara shirye-shiryen yiwa Senatan su kiranye ta hanyar da dokar kasa ta aminta dashi.

Izuwa yanzu dai wadanda suka jefa wa Senata Suleiman Hunkuyi kuri’u a zaben da ya gabata sun fara janye kuri’ar su domin dawo dashi gida daga aiken da suka yimasa zuwa majalisa. 

A cewar masu kiranyen, kiranyen ya biyo bayan rashin iya wakilci da kuma kaucewa akan abunda suka wakilta shi yaje majalisar ya aiwatar.

In dai ba mu manta ba, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bawa masu zabe damar janye kuri’ar su akan senata ko dan majalisar wakilai da suka tura majalisa muddin bukatar hakan ta taso.

You may also like