An fatattaki ‘yan luwadi a Uganda


‘Yan sanda sun fatattaki masu luwadi daga wuraren da suke sheke aya.
An dai ce ‘yan luwadin suna shagalin bikin aure ne a wasu wurare guda biyu a da ke kusa da tafkin Lake Victoria, a Kampala.

Daman dai ministan samar da Da’a da kare mutunci na kasar, ya sha alwashin daukar tsauraran matakai kan shagulgulan na masu luwadi.

A shekarar 2014 ne dai aka soke batun yin dokar da za ta ba sanya yin luwadi a jerin aikata manyan laifuka, a Uganda.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like