An Fitar da sabon vidiyon ‘yan matan Chibok


Kungiyar Boko Haram ta saki wani sabon faifan bidiyo wanda ta ce yana dauke da ‘yan matan Chibok da ta sace sama da shekaru biyu da suka wuce a garin chibok dake Jihar Bornon Najeriya.
Kimanin ‘yan mata 50 ne aka nuna sanye da hijabai inda suke zaune a bayan wani mutum dauke da bindiga, wanda ya nemi a saki mayakan kungiyar kafin su saki ‘yan matan.Mutumin wanda ya rufe fuskarshi, ya ce wasu daga cikin ‘yan matan sun mutu a hare-haren da sojin Najeriya suka kai ta sama.

An sace ‘yan matan ne su 276 daga makarantarsu a garin Chibok, kuma har yanzu Boko Haram na cigaba da tsare fiye da 200.Wannan ne karo na uku da aka wallafa bidiyon da ke nuna ‘yan matan tun bayan da aka kama su.

Mutumin da ya fara magana a bidiyon ya ce an jikkata wasu daga cikin ‘yan matan, sannan wasu na kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.Sannan ya ce an “aurar” da kusan 40 daga cikinsu.Ya kara da cewa “muna bukatar gwamnati ta saki mayakanmu, idan ba haka ba, ba za mu taba sakin wadannan ‘yan matan ba”.

Faifan bidiyon ya nuna wani dan kungiyar yana yin hira da daya daga cikin ‘yan matan, wacce ta kira kanta Maida Yakubu, sannan ta ce daga Chibok ta ke.

Mutumin ya sa ta nemi gwamnati da ta saki mayakan kugiyar da take tsare da su.”Ina neman iyayenmu da su bugi-kirji, su yi magana da gwamnati domin a kyalemu mu koma gida,” kamar yadda ta fada a harshen Kabaku.Ana iya hango daya daga cikin ‘yan matan wacce ke zaune a baya rike da wani jariri.

Ana fargabar cewa da dama daga cikin yaran an yi lalatada su, yayin da wasu kuma aka tilasta musu aurar wadanda suka kama su.Bidiyon na kuma dauke da gawarwakin mutane, wadanda kungiyar ta ce sojojin Najeriya ne suka kashe a hare-haren da suke kaiwa ta sama.

Boko Haram ta shafe shekaru bakwai tana yaki da gwamnatin Najeriya, kuma a kwanan ne wani bangarenta ya balle inda ya koma karkashin kungiyar ISIS mai ikirarin kafa daular Musulunci.

Dubban mutane Boko Haram ta kashe ko ta kama a ‘yanshekarun da suka gabata, yayin da fiye da mutane miliyan biyu suka tsere daga gidajensu

You may also like